ABNA24 : Da yake sanar da hakan shugaban kwamitin kula da zabe na kasar, Jamal Orf, ce babu gamshin gaskia game da rade raden cewa za’a jinkirta zaben shugaban kasar dake tafe.
Za’a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara tunda farko a ranar 18 ga watan Yuni 2021.
Mista Orf, ya ce game da halin da ake ciki na annobar korona, y ace tuni aka tsara dukkan matakan da suka wajaba domin kare lafiyar ma’aikatan zabe da kuma masu zabe.
Game da zabukan wakilan kananen hukumomi za’a gudanar da su ne ta kafar intanet, wanda kuma shi ne karon farko a tarihin kasar.
Kawo yanzu dai jam’iyyun siyasa na ci gaba da tantance ‘yan takaran da zasu tsaida a zaben shugaban kasar wanda shi ne karo na 13, bayan cimma nasara juyin juya halin musulinci a kasar shekaru 42 da suka gabata.
342/